Yanzu Yanzu: Kalli yadda rundunar sojin sama ta tayar da mafakar yan ta’adda a Borno, ta kashe mayakan Boko Haram da dama (bidiyo)

Yanzu Yanzu: Kalli yadda rundunar sojin sama ta tayar da mafakar yan ta’adda a Borno, ta kashe mayakan Boko Haram da dama (bidiyo)

Rahotanni sun kawo cewa yan ta'addan Boko Haram da dama sun hallaka baan jiragen yaki mallakar rundunar sojin saman Najeriya a Operation Lafiya Dole sun kai hari mabuyyarsu.

A wani jawabi daga rundunar sojin saman, tace aikin rundunar saman na Operation Lafiya Dole ya kasance cigaban kakkabe yan ta'adda dake gudana a yankin aewa maso gabashin kasar.

A cewar jawabin, wadanda aka kaiwa harin na cikin mayakan ISWAP a Bukar Meram dake tafkin Chadi a yankin arewacin jihar Borno.

Jawabin wanda Air Commodore Ibikule Daramola, daaktan labarai na runduna ya saki, ya nuna cewa an gudanar da aikin ne a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba.

Ta kara da cewa an gudanar da aikin ne bisa ga bayanan kwararru da ya nuna cewa an dawo da amfani da wajen domin ba yan taáddan tallafin kayayyaki, ta hanyar amfani da ayyukan kamun kifi a matsayin rufi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar sojin saman Najeriya (NAF) tace tana bincike akan wani rahoton yanar gizo dake zargin jami’inta da kashe mutane biyu a yankin Mabera da ke jihar Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya ta sake kama wasu manyan kwamandojin Boko Haram a Borno

Darektan labarai da hulda da jama'a na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a wani jawabi a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba a Abuja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel