Kudin da ake kashewa mai laifi dake kurkuku a Amurka a kullum yafi albashin da ake bawa ma'aikacin gwamnatin Najeriya a wata - Ministan cikin gida

Kudin da ake kashewa mai laifi dake kurkuku a Amurka a kullum yafi albashin da ake bawa ma'aikacin gwamnatin Najeriya a wata - Ministan cikin gida

- Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ya bayyana cewa kudin da ake kashewa dan gidan kurkuku a kasar Amurka a kullum yafi albashin da ake bawa ma'aikacin gwamnati a Najeriya

- Ya bayyana cewa akwai jihohin da ake kashewa dan gidan kurkuku naira dubu sittin a kowacce rana, yayin da shi kuma ma'aikacin Najeriya ake biyan shi albashin naira dari bakwai da talatin a kullum

- Ya ce Najeriya ba ta da karfin arziki kamar kasar Amurka, amma kamata yayi gwamnati ta inganta rayuwar ma'aikatan ta

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ya baiwa 'yan Najeriya mamaki, yayin da yace kudin da ake kashewa mai laifi wanda yake kurkuku a kasar Amurka a kullum yafi albashin da ake bawa ma'aikacin gwamnatin Najeriya a wata daya.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen gabatar da kasafin kudi na ma'aikatar shi a gaban kwamitin Sanatoci da aka gabatar.

Haka kuma ya bayyana cewa karancin abinda ake kashewa mai laifi dake gidan kurkuku a kasar Amurka a kullum naira dubu talatin da daya ne (N31,000), wanda shi kuma ma'aikacin gwamnati dake daukar karancin albashi yake samun naira dari bakwai da talatin (N730) a kowacce rana.

KU KARANTA: Tashin hankali: Na yi mankas da kwaya ne har naje na kashe mahaifina ban sani ba

Ministan wanda yayi Allah wadai da tattalin arzikin Najeriya dama 'yan Najeriya baki daya, daga baya ya gano cewa ma a wasu jihohin na kasar Amurka ana kashewa 'yan gidan kurkuku naira dubu sittin a kowacce rana (60,000).

A cewar shi, tattalin arzikin Najeriya bai kai na kasar Amurka karfi ba, hakan yasa dan gidan kurkuku yafi ma'aikacin gwamnatin Najeriya jin dadi.

"Hada Najeriya da kasashe irin su Amurka, Turkey dama Egypt zai cirewa ma'aikatan Najeriya kaunar aikin gwamnati kwata-kwata, amma abinda ya kamata muyi shine, da dan arzikin da Allah ya bamu, mu samu mu inganta rayuwar ma'aikatan mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel