Rundunar sojin Najeriya ta sake kama wasu manyan kwamandojin Boko Haram a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta sake kama wasu manyan kwamandojin Boko Haram a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta kama kwamandojin Boko Haram guda biyu Lawan Abubakar Umar Garliga da Bayaga Manye.

Rudunar hadin gwiwa da suka hada da dakarun Brigade 26, Brigade 21 da yan sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) ne suka kama kwamandojin biyu yayinda suke gudanar da aiki kan wani bayanin kwararru.

A wani jawabi daga rundunar sojin ta bayyana cewa tawagar ta gudanar da ayyuka akan yan ta'addan yayinda suke zarya a kewayen yankin Pulka na karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba.

Aikin yayi sanadiyar kama wasu mambobin kungiyar Boko Haram guda 16.

Mayakan kungiyar da aka kama na daga cikin yan Boko Haram 41 da 90 da rundunar sojin Najeriya ke nema ruwa a jallo.

Kamun kwanan nan ya kasance cikin kokarin da gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ke yi don ganin an inganta amfani da hanyoyi da dama na yakan yan Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama na bincike kan zargin da ake yiwa jami’inta na kashe mutum 2 a Sokoto

Gwamnan a lokacin da ya kai ziyara zuwa kananan hukumomi 27 dake jihar, hade da Bama, sun yi ganawa da yan bangan JTF, da masu farauta da kuma samar musu motoci da sauran kayan aiki da suke bukata don gudanar da aiki.

A ranar Litinin Zulum ya zanta da mambobin majalisarsa a Damasak, wani tsohon yankin da yan Boko Haram suka addaba da kuma hedikwatan karamar hukumar Mobbar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel