Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu

Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu

Babban kotun tarayya dake Abuja ta bada umurnin sadaukarwa gwamnatin tarayya dukiyoyi 23 da ake kyautata zaton na tsohon shugaban gyara harkan fansho, Abdulrashid Maina.

Alkali Folashade Ogunbanjo, ta bayyana umurnin ne ranar Talata yayinda take yanke hukunci kan karar da hukumar hana almundana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

A karar, hukumar yaki da rashawan ta bukaci kotun ta sadaukarwa gwamnati dukiyoyin dake da alaka da Maina.

Hakazalika ta bukaci izinin gwamnati ta wallafa dukkan dukiyoyin a jaridu saboda duk wanda ke da hujjan cewa dukiyarsa ya fito ya kawo hujja.

Alkalin ta bada EFCC umurnin cewa a dawo kotu ranar 19 ga Nuwamba domin cigaba da karar.

A cewar EFCC, dukiyoyin da aka sadaukar na jihohin Kaduna, Borno, Sokoto da birnin tarayya Abuja.

Kalli jerin dukiyoyin:

Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu
jerin
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bayan shekaru aru-aru, an fara hada fensir a Najeriya

Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu
Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu
Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel