Rundunar sojin sama na bincike kan zargin da ake yiwa jami’inta na kashe mutum 2 a Sokoto

Rundunar sojin sama na bincike kan zargin da ake yiwa jami’inta na kashe mutum 2 a Sokoto

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) tace tana bincike akan wani rahoton yanar gizo dake zargin jami’inta da kishe mutane biyu a yankin Mabera da ke jihar Sokoto.

Darektan labarai da hulda da jama'a na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a wani jawabi a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba a Abuja.

“Wani rahoton yanar gizo ya yi zargin kisan mutane biyu a Mabera dake bornin Sokoto a jiya, 20 ga watan Oktoba sakamakon rikici da ya barke tsakanin jami’in rundunar sojin saman Najeriya da wani matashi dan kungiyar matasan Shi'a a tsakanin garin.

“Sai dai, ba a samu cikakken bayani game da lamarin ba, wanda yayi sanadiyyar raunata wasu jami’an NAF.

“Bugu da kari, NAF tana gudanar da bincike kan lamarin, tana kuma burin gano gaskiya da kuma abunda ya kawo jami’anta cikin lamarin.

KU KARANTA KUMA: Tawagar hazikin dan sanda Abba Kyari sun kama masu garkuwa da mutane 81

“Muna tabbatar ma al’umma da cewar, kamar yanda rundunar sojin sama ta saba aiwatarwa, zata tabbatar da kammala cikakken bincike sannan zata dauki matakin da ya kamata.

"Don haka duk jami'in sojan da akan kama da laifin cin zarafi a baya, sun fuskanci hukunci daidai da doka kuma ana sanar da jama'a hakan."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel