Ganduje ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Ganduje ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa

- Duk da banbancin siyasa da ke tsakanin Ganduje da Kwankwaso, Gwamna ya aje shi gefe don yi wa wanda ya gadan muranar zagayowar ranar haihuwarsa

- Gwamnan ya taya tsohon sanatan murnar ne a shafi mai lamba 41 na jaridar Daily Trust ta ranar Talata

- A madadin gwamnan, gwamnatin jihar Kano da daukacin al'ummar jihar, an yi wa Kwankwaso addu'ar lafiya mai dorewa da yalwatar arziki

Gwamnan jihar Kano, Dr Umar Abdullahi Umar Ganduje, ya taya wanda ya gada, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murnar ranar zagayowar haihuwarsa.

A shafin talla mai lamba 41 na jaridar Daily Trust ta ranar Talata, Ganduje ya yi wa Kwankwaso fatan zagayowar shekarun masu zuwa cikin farinciki tare da addu’ar lafiya da yalwatar arziki.

KU KARANTA: Karancin albashi: Ma'aikatar kwadago ta sanar da lokacin da za a fara biya

“Ni Abdullahi Umar Ganduje, a madadina, gwamnatin jihata da mutanen jihar Kano, muna taya tsohon gwamnan jihar kuma tsohon sanata , Rabiu Musa Kwankwaso, murnar zagayowar ranar haihuwarsa karo na 63,”

“A yayin da muke mishi fatan shekarun masu albarka nan gaba, muna addu’ar Allah ya bashi lafiya mai dorewa da yalwatar arziki” Ganduje ya yi addu’ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel