Badakalar N25bn: Kotu ta bukaci ICPC ta kawo mata ministan Buhari

Badakalar N25bn: Kotu ta bukaci ICPC ta kawo mata ministan Buhari

- Kotun tarayya da ke Abuja ya yi barazanar watsi da karar da ICPC ta shigar kan shugaban NBC, Ishaq Modibbo Kawu

- Kotun ta ce muddin ICPC ba ta kawo ministan sadarwa Lai Mohammed da wani dan canji da za su bayar da shaida ba za tayi watsi da karar

- Ana tuhumar shugaban na NBC ne da bannatar da zunzurutun kudi naira biliyan 2.5 na kwangilar sauya hanyoyin sadarwa zuwa na zamani wato digital

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a jiya Litinin ta bawa Hukumar yaki da rashawa ta ICPC gargadi na karshe ta kawo Ministan Sadarwa, Lai Mohammed kotu ya bayar da shaida kan shari'ar da ke yi kan shugaban hukumar watsa labarai na kasa NBC, Ishaq Moddibo Kawu da wasu mutane biyu da ake zargin sun bannatar da N2.5 biliyan da gwamnati ta ware na sauya hanyoyin sadarwa na hukumar zuwa digital.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

Mai shari'a Folashade Ogunbanjo-Giwa ya ce ministan da wasu mutane biyu sune shaidu biyu da suka yi saura da ba su hallarci kotun ba a kan shari'ar Kawu da Pinnacle Communications Ltd, Lucky Omoluwa da Dipo Onifade a kan zargin da ICPC ke musu da bannatar da kudin kwangila.

Mai shari'a Ogunbanjo-Giwa ya yi gargadin cewa idan ICPC ta gaza kawo ministan da kuma wani dan canji da shima bai hallarci kotun ba a baya, hakan zai iya saka kotun tayi watsi da karar.

A baya, lauyan wanda suka shigar da kara, Ephraim Otti ya shaidawa kotun cewa dan canjin baya kasar kuma ministan shima ba zai samu daman zuwa kotun ba kuma ya nemi a sake daga sauraron shari'ar.

A bangarensu, lauyoyin wanda aka yi kara, Akeem Mustapha (SAN), Jovi Oguejiofor da Ama Etuwewe (SAN) ba su amince da bukatar sake daga cigaba da sauraron shari'ar ba.

Daga karshe dai kotun ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranakun 3, 4 da 5 na watan Disamba domin bawa wanda suka shigar da kara damar gabatar da sauran shaidunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel