EFCC za ta gurfanar da Maina da 'dan sa a kotu ranar Juma'a

EFCC za ta gurfanar da Maina da 'dan sa a kotu ranar Juma'a

- Za a gurfanar da Mista Abdulrasheed Maina da 'dansa Faisal Maina a gaban kotu a ranar Juma'a

- Ana zargin Maina da aikata laifuka da dama masu alaka da karkatar da kudade da almundaha a yayin da ya ke shugaban hukumar fansho ta kasa

- Mista Maina ya kwashe shekaru hudu yana zilewa jami'an tsaro amma a ranar 30 ga watan Satumba jami'an DSS suka damke shi a wani otel a Abuja

Za a gurfanar da tsohon shugaban hukumar fansho Abdulrasheed Maina da dansa Faisal Maina a gaban Mai shari'a Abang Okon na kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a kan tuhume-tuhume daban-daban.

Duk da cewa a yanzu ba a san takamamen laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba, ana kyautata zaton hukumar yaki da rashawar ta gabatar karraki daban-daban kan Maina da dansa.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

A ranar 30 ga watan Satumban 2019 ne jami'an 'yan sandan farar hula, DSS suka kama Mista Maina da dansa a wani Otel da ke birnin tarayya Abuja kuma daga bisani suka mika su hannun hukumar EFCC a ranar 2 ga watan Oktoba don a zurfafa bincike kan tuhumar almundaha da karkatar da kudi da ya kai naira biliyan 2.1.

Mista Maina ya kwashe shekaru hudu yana zilewa jami'an tsaro kafin daga baya 'yan sandan farar hula suka samu nasarar damke shi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Hukumar EFCC ta samu izinin tsare Mista Maina da 'dansa na tsawon kwanaki 14 a ranar 7 ga watan Oktoba daga wurin Kotun tarayya da ke Bwari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel