'Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 17 a jihar Kaduna

'Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 17 a jihar Kaduna

- 'Yan ta'adda dauke da miyagun makamai sun tarwatsa kauyuka 17 na wata karamar hukumar da ke jihar Kaduna

- Mutane 2,000 ne suka tsere daga kauyukan inda suka samu mafaka a wata makarantar firamare

- A halin yanzu jami'an tsaro na bin sawun 'yan ta'addar inda wasu kuma ke tsaron 'yan gudun hijirar

A wani rahoton gidan talabijin din Channels, sun nuna yadda 'yan ta'adda dauke da miyagun makamai suka afka kauyuka 17 na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kamar yadda rahoton ya nuna, abun alhinin ya auku ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba. Abinda yasa mazauna kauyukan suka yi gudun hijira don tseratar da rayukansu.

KU KARANTA: Karancin albashi: Ma'aikatar kwadago ta sanar da lokacin da za a fara biya

An zargi cewa, 'yan bindigar sun hallaka 'yan banga ukun da suka shiga daji don tararsu.

Rahoton ya nuna cewa, mutanen da suka yi gudun hijirar sun kai mutane 2,000 kuma a halin yanzu suna wata makarantar firamare inda suka samu mafaka.

Wani babban jam'in hukumar 'yan sanda ya sanar da jaridar The cable cewa, jami'an tsaro sun bazama don kamo 'yan ta'addan.

"Rundunar jami'an tsaro a halin yanzu na bin sawun 'yan ta'addan inda wasu ke bawa 'yan gudun hijarar tsaro a makarantar firamaren Ba dake kan titin Kaduna zuwa Zaria. Hakan kuwa zai sa hankulan 'yan gudun hijrar ya kwanta don komawa gidajensu." in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel