Kotu ta rufe cocin Anambra saboda yawan hayaniya

Kotu ta rufe cocin Anambra saboda yawan hayaniya

Babbar kotun Majistare Nnewi ta rufe wani coci a yankin Nnewi, jihar Anamba kan zargin yawan hayaniya.

Daraktan ma’aikatar lafiyar muhalli, Nnewi da hana afkuwar fitina na karama hukumar Nnewi ta arewa ne ya maka cocin a kotu.

A karar mai lamba NMC/10c/2019, ana karar cocin kan tuhume-tuhume biyu karkashin dokar lafiyar jama’a na jihar Anambra.

An zargi cocin da amfani da wani abun sautin murya da kuma sanya sifiku biyar a gaban harabarta wanda hakan ke haifar da hayaniya da damun jama’a dake makwabtaka da su.

Lauyan gwamnati ya bayyana lamarin a matsayin hatsari ga lafiyar dan adam wanda daidai yake da hukunta mutum a sashi na 21 na dokar lafiyar jama’a a jihar Anambra 2006.

An kuma zargi cocin da rashin bayar da hadin kai ga ka’idoji da takardar jan hankali mai lamba No: 00000896 da aka gabatar mata.

Lauyan gwamnatin yace lamarin daidai yake da hukunci a sashi na 8(1,4b) da 9(1,2) na dokar lafiyar jama’a a jihar Anambra.

Ya kuma gabatar da shaidu uku wadanda suka tabbatar da cewar ayyukan cocin, musamman lokacin addu’o’in dare, na damun mutane, ciki harda wata tsohuwa yar shekara 86.

Sai dai Shugaban garin, wanda ya bayyana a matsayin shaidar wanda ake kara, yace ayyukan cocin bai damu kowa ba.

KU KARANTA KUMA: TEI-INEC: Alamu sun nuna cewa za a iya samun rikici a zaben Jihar Kogi

Da yake zartar da hukunci kan lamarin, kotun karkashin jagorancin A.C. Emekwue ya umurci daraktan lafiyar muhalli da ya rufe cocin.

Kotun ta kuma umurci wanda ake karan da ya dauke cocin daga wajen cikin kwanaki 10 ko kuma ya fuskanci daurin shekara daya ba tare da tara ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel