Saraki ya yi martani kan kwace kadarorinsa da kotu tayi

Saraki ya yi martani kan kwace kadarorinsa da kotu tayi

A jiya Litinin ne babban kotun tarayya da ke Legas ta bayar da umurnin kwace wasu gidaje biyu mallakar tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki a unguwar Ikoyi a Legas.

Mai shari'a Mohammed Liman ya bayar da umurnin karbe kadarorin bayan karar da Hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annti EFCC ta shigar a kotun.

A martanin da ya yi a daren jiya, Saraki ya ce babu shakka hukumar EFCC ta gabatarwa kotu bayyanai marasa sahihanci kafin bayar da umurnin don ba a sanar da shi ko lauyoyinsa cewa an shigar da karar ba a gaban kotu.

Hukumar ta EFCC ta ce, ta ce tana kyautata zaton "Filin mai lamba 17A a MacDonald Road, Ikoyi," an saye shi ne da kudin da aka samu ta haramtattun hanya.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

A shaidan da ta gabatar kan Saraki, EFCC ta ce 'Saraki ya cire kudi sama da naira biliyan 12 daga asusun gwamnatin jihar Kwara sannan ya tura kudin zuwa wasu asusunsa biyu ta hannun hadiminsa, Abdul Adama a lokuta daban-daban."

Lauyan EFCC, Nnaemeka Omewa ya ce kotun ta bayar da ikon kwace filayen a kuma mika wa gwamnatin tarayya.

Mai shari'a Liman ya amince da hakan.

Bayan bayar da umurin, Mai shari'a ya umurci EFCC ta wallafa umurnin a jaridun kasa.

An bawa Saraki kwanaki 14 ko duk wani da ke da hujjar nuna cewa shi ya mallaki filayen ya gurfana gaban kotu ya gabatar da hojjojinsa kafin kotu ba bawa gwamnati umurnin rike filin dindindin.

A sakon da ya fitar da hannun hadiminsa, Yusuph Olaniyonu, Saraki ya ce wata kotun Abuja ta bayar da umurnin kada a dauki wani mataki kan wadannan filayen domin ana shari'a a kansu dama.

Ya ce kotun na Abuja ta ce ba shi da wani tambayoyi da zai amsa kan filayen saboda haka ya yi nasara a kan batun.

Ya yi kira ga abokai da magoya bayansa su kwantar da hankulansu domin wannan umurnin ba mai dorewa bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel