TEI-INEC: Alamu sun nuna cewa za a iya samun rikici a zaben Jihar Kogi

TEI-INEC: Alamu sun nuna cewa za a iya samun rikici a zaben Jihar Kogi

Sashen TEI da ke karkashin hhukumar INEC mai zaman kanta, ta kyankyasa cewa alamun farko sun gama nuna cewa za a samu rikici wajen zaben gwamnan jihar Kogi da ake shirin gudanarwa.

Shugaban TEI, Prince Solomon Adedeji Soyebi, ya bayyana wannan a lokacin da aka shriya wani zama game da zaben na jihar Kogi. An yi wannan zama ne a Garin Abuja a Ranar 21 ga Oktoba.

Prince Solomon Adedeji Soyebi ya kuma nuna cewa an fara shirin sayen kuri’un jama’a ban da tanadin rigimar da ake yi. Shugaban sashen ya yi albishiri cewa za su takawa shirin burki.

“Abin da za mu yi shi ne mu yi kokarin hana saida kuri’a ta hanyar hana kowa ganin abin da mutum ya zaba. Idan aka yi haka, babu wanda zai bada kudi bayan ka kada kuri’a a zabe.” Inji sa.

KU KARANTA: INEC ta bayyana ranar da za a sake zaben Sanatan Kogi ta Yamma

A cewar Mista Adedeji Soyebi: “Mun fada, mun nanata cewa saida kuri’a bai halatta ba. Jami’an tsaro su na cigaba da hukunta masu yin wannan danyen aikin kuma za a cigaba da hukunta su.”

Darekta Janar na TEI, Dr. Sa’ad Idris, ya ce an shirya wannan taro ne domin bibiyar irin shirin da hukumar zaben kasar ta yi. A Ranar 16 ga Watan Nuwamban 2019 ne za a gudanar da zaben.

Da yake jawabinsa, Sa’ad Idris ya bayyana cewa makasudin taron shi ne a san wuraren da za ayi gyara domi ganin an shirya zabe na gaskiya da adalci fiye da abin da aka shirya a lokutan baya.

Gwamna Yahaya Bello wanda yake kan mulki zai kara ne da ‘dan takarar PDP, Injiniya Musa Wada. Jam’iyyar PDP ta na kokarin karbe jihar da ta rasa a 2015, yayin da Bello ke harin zarcewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel