An bankado yunkurin tserar da tsohon shugaban hukumar fansho, Maina

An bankado yunkurin tserar da tsohon shugaban hukumar fansho, Maina

- An cafke jami'an hukumar yaki da rashawa ta EFCC 7 da zargin yunkurin fidda Maina daga ma'adanar hukumar

- An zargi cewa, Zainab ta hada baki da wasu ne don kubutar da Maina daga inda EFCC ta adanashi

- Tuni aka cafke jami'an da ke aiki a wajen tare da Zainab don amsa tambayoyi akan zargin da ake musu

An cafke jami'an hukumar yaki da rashawa ta EFCC 7 akan zarginsu da ake da yunkurin fitar da tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, AbdulRasheed Maina daga inda hukumar ta adana shi.

Ana tuhumarsu ne tare da wata mata mai suna Zainab Abbas don gano gaskiyar lamarin.

Hukumar ta sakaya Maina ne sakamakon tuhumarsa da take masa da wawurar naira biliyan 2.1 na hukumar fansho.

KU KARANTA: Pantami ya samu lambar yabo

Hukumar ta zargi cewa, Zainab Abbas, wacce ta ziyarci Maina a jiya Litinin ce shugabar yunkurin fitar da Maina.

Kamar yadda majiyar ta sanar, jami'an 7 na EFCC na aiki a lokacin da aka yi yunkurin aiwatar da aika-aikar.

Majiyar ta kara da cewa: "Mun samu bayanan sirri akan hakan tun a ranar 17 ga watan Oktoba. A daren jiya ne aka shigar da wata Zainab Abbas zuwa farfajiyar baki don ganawa da Maina. Tana kuma tare da wayarta ne."

"An zargi cewa, tayi ta kokarin kiran wasu jami'an soji don fitar da Maina din. A take, an kasa gano cewa ko akwai hannun Maina a yunkurin ko kuma wasu ne suka yi hayar Zainab Abbas,"

"Tuni aka cafke jami'an da ke aiki ranar tare sakayasu. Ana kuma bincikarsu don ganowa ko da hadin bakinsu,"

"Amma kuma tun farko, an bar Zainab yin amfani da wayarta duk da kuwa doka ce ba a shiga da waya don ganin wanda ake zargi."

Majiyar ta kara da cewa: "Mukaddashin shugaban EFCC ya bada umarnin kara jami'an tsaro a inda Maina yake tsare. Duk baki daga yanzu kuma zasu bi dokar hukumar ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel