Tashin hankali: Na yi mankas da kwaya ne har naje na kashe mahaifina ban sani ba

Tashin hankali: Na yi mankas da kwaya ne har naje na kashe mahaifina ban sani ba

- Wani saurayi da ya kashe mahaifinsa har lahira ya bayyana cewa ya sha kwaya ne ya bugu yaje ya kashe shi

- An bayyana cewa rikici ne ya kaure tsakanin saurayin da mahaifinsa kawai sai ya fara dukan shi har yayi amfani da wata kwalba ya caka masa, shi kuwa ya ce ga garinku nan

- Dama dai an ce ba wannan ne karo na farko da suka fara wannan rikici ba, sun saba yin irin hakan

Wani saurayi dan shekara 20 a duniya ya shiga hannun jami'an 'yan sanda bayan an kama shi da laifin dukan mahaifinsa mai shekaru 65 har yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Umuaro dake cikin karamar hukumar Ehime Mbano dake cikin jihar Imo.

Matashin saurayin wanda aka bayyana sunansa da Ikechukwu Munahawu, ya kashe mahaifinsa mai suna Mr. Patrick Munahawu da wata fasasshiyar kwalba, sai dai kuma ya bayyana cewa yayi wannan aika-aika ne saboda kwayar da ya sha.

KU KARANTA: Wata kyakkyawar budurwa ta mutu bayan aminiyarta ta saka mata guba a abinci saboda ta samu karin girma a wajen aiki

Wani jami'in dan sanda da yake aiki a ofishin 'yan sanda dake Ehime Mbano, ya nemi a boye sunansa, ya ce marigayin ya mutu ne bayan wani rikici da suka yi da babban dan nasa.

Haka kuma wasu rahotannin sun bayyana cewa 'yan uwan marigayin sun bayyana cewa matashin saurayin ya sha yin rikici da mahaifin nasu ya dinga marin shi akan idon kannanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel