An karrama Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano

An karrama Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano

- Wata kungiyar wasanni ta karrama Gwamnan Abdullahi umar Ganduje na jihar Kano

- Kungiyar ta jinjinawa gwamnan ne sakamakon rawar da yake takawa wajen habaka fannin wasanni a jihar Kano din

- Hakan kuwa na da matukar muhimmanci ga matasan jihar domin kuwa ya jawo farfadowar kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillars

Wata kungiyar wasanni ta yi bayanin dalilin da yasa ta karrama Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kungiyar, wacce ta bawa gwamnan lambar yabo tare da wasu mutane 9 a wani bikin murna da ya gudana a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna. Ta ce, ta karrama gwamnan ne sakamakon taka rawar ganin da yake yi ta bangaren wasanni a jihar Kano.

KU KARANTA: Yanzu- yanzu: Zaki ya kwace daga ma'adanarsa a gidan zoo din Kano

Shugaban kungiyar, Baba Danlami, ya ce, tun daga hawa mulkin gwamnan, bangaren wasanni a jihar Kano din ta samu cigaba.

Gwamnan ya nuna damuwarsa akan bangaren wasannin wanda a sakamakon hakan ne kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta farfado.

Ya ce, matasa a jihar Kano sun samu cigaba ta bangaren wasanni.

Yayin karbar lambar yabon a maimakon gwamnan, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya mika godiyarsa ga matasan akan jinjinar da suka yi wa gwamnan. Ya ce, hakan na nuna cewa matasan suna jin dadin kokarin gwamnan ta bangaren habaka jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel