Zaben Bayelsa: Zamu share muku takaicin PDP idan kuka zabe mu, inji Oshiomole

Zaben Bayelsa: Zamu share muku takaicin PDP idan kuka zabe mu, inji Oshiomole

Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ya ce, jam’iyyarsa za ta gyara duk wani kuskuren da PDP ta tafka a Bayelsa idan har aka zabe su a zaben gwamnan dake tafe wata mai zuwa.

Oshiomole ya fadi wannan maganar ne a wurin taron bude kamfen APC a karamar hukumar Ogbia dake jihar Bayelsa.

KU KARANTA:Majalisar dokoki ta bankado wata badakkalar biliyoyin kudi a karkashin hukumar NIWA

Shugaban APC ya ce, jam’iyyar ta kafa tawagar mutane masu nagarta, a don haka babu abinda suke dubi in banda nasara a zaben 16 ga watan Nuwamba na gwamnan jihar.

Oshiomole ya ce: “APC ta zo ne domin ta gyara kusakuren PDP a jihar Bayelsa. Gwamnatin APC a karkashin David Lyon za ta yi aiki tukuru domin samar da tsaro, aikin yi da kuma bunkasa mutane a Bayelsa.”

Shugaban APC ya cigaba da cewa, nasarar jam’iyyarsa a zaben gwamnan dake tafe zai sake dawo da martabar jihar da jama’a suka rasa a sakamakon rashin jagoranci mai kyau.

Daga cikin kalamansa, har ila yau, Oshiomole ya ce, ba wai takura ko bin diddigin gwamnatin PDP ke gabansu illa gyaran kusakuran da gwamnatinsu ta tafka a jihar Bayelsa.

A na shi jawabin kuwa, dan takarar gwamnan karkashin jam’iyyar ta APC, David Lyon ya ce, ba zai yi alkawari yaki cikawa ba.Ya kuma kara da cewa zai yi amfani da kudorin da zasu kawowa jihar Bayelsa.

A cikin jawabinsa, ya fadi cewa zai farfado da wannan katafaren kamfanin samar da wutar lantarki a jihar ta Bayelsa.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/guber-poll-apc-ll-correct-pdps-mistakes-in-bayelsa-if-elected-oshiomole/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel