Za mu sake zaben Sanatan Kogi ta Yamma a Ranar Nuwamba 16 - Okoye

Za mu sake zaben Sanatan Kogi ta Yamma a Ranar Nuwamba 16 - Okoye

Hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya watau INEC, ta bayyana ranakun da ta shirya domin sake gudanar da zaben kujerar majalisa a wasu jihohin kasar da aka bukaci a sake shirya zaben.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Festus Okoye, ya zanta da Manema labarai jiya 21 ga Watan Oktoba a Garin Abuja inda ya bayyana jadawalin da aka fitar.

A cewar Mista Festus Okoye, za a shirya sabon zaben kujerar majalisar dokokin jihar Katsina a shiyyar Sabuwa a Ranar 39 ga Watan Nuwamba, 2019. An kuma sa ranar zaben da za ayi a Kogi.

Kwamishinan na INEC yake cewa za a yi zaben kujerar ‘dan majalisar dattawa na Mazabar Kogi ta Yamma ne a Ranar 16 ga Nuwamba. Wannan ya fado rana daya da ake zaben gwamna a jihar.

KU KARANTA: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi ya bayyana wahalar da ya sha

Idan ku na biye da mu, kun san cewa za a yi danyen zabe a jihohin Katsina da Kogi bayan rasuwar Honarabul Mustapha Abdullahi, sannan kuma babban kotu ta soke zaben Sanata Dino Melaye.

Majalisar dokokin jihar Katsina ta aikawa INEC takarda a cikin watan Satumba inda ta sanar da ita mutuwar ‘dan majalisar da ke wakiltar yankin Sabuwa wanda ya rasu bayan ya lashe zabe.

INEC ta maidawa wasikar majalisar ta Katsina mai lamba KTSHA/PER/HON/l24/VOL.l/24 amsa da cewa za a soma gudanar da zaben fitar da gwanin jam’iyyu ne daga Ranar 24 ga Watan Oktoba.

A Ranar 6 ga Nuwamba za a kammalla shirin tsaida ‘dan takara, sannan a aikawa hukuma sunayen wadanda aka zaba. INEC ta nemi jam’iyyun su yi yakin neman zabe ba tare da rikici ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel