Shugabannin APC sun jinjinawa Buhari saboda shirin binciken hukumar NDDC

Shugabannin APC sun jinjinawa Buhari saboda shirin binciken hukumar NDDC

Manyan kungiyar shugabannin jam’iyyar APC a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudancin kasar nan sun fito su na jinjinawa umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada a NDDC.

Jagororin jam’iyyar APC mai mulkin kasar sun ji dadin matakin da shugaban kasar ya dauka kwanan nan na bin diddikin abin da hukumar NDDC ta ke yi da irin makudan kudin da ake ba ta.

Wannan kungiya ta ‘Ya ‘yan APC ta na ganin cewa kwamitin da aka kafa ya yi wannan aiki zai yi kokari domin kuwa babu wani tsohon shugaba ko babban Darektan NDDC a cikin ‘yan kwamitin.

"Za su yi bakin kokari na ganin kawo gyare-gyare a hukumar tare da magance matsalolin da ake fuskanta na tabarbarewar abubuwan more rayuwa a yankin na Neja-Delta." inji shugabannin APC.

KU KARANTA: An fara zargin Gwamnan Ebonyi da hada-kai da Buhari a boye

Jagororin jam’iyyar sun fitar da jawabi ne a mabanbantan lokuta. Shugaban jam’iyyar na jihar Akwa-Ibom kuma Jagoran jam’iyyar a yankin Neja-Delta watau Ini Okopido ya fitar da jawabi.

Haka zalika Donatus Nwankpa wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na jihar Abia, kuma jagora a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriyar, ya fitar da na sa jawabin a madadin ‘ya ‘yan jam’iyya.

Kusoshin na APC sun ji dadin wadanda shugaba Buhari ya nada domin su jagoranci ragamar cigabar yankin mai arzikin man fetur. Su na ganin cewa an zakulo wadanda su ka san kan aiki.

Jam’iyyar ta kuma ji dadin yadda shugaban kasar ya damu da yankin, inda ita ma ta bayyana za ta cigaba da bada goyon baya wajen ganin an yi wa hukumar ta NDDC ta Neja-Delta garambawul.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel