Majalisar dokoki ta bankado wata badakkalar biliyoyin kudi a karkashin hukumar NIWA

Majalisar dokoki ta bankado wata badakkalar biliyoyin kudi a karkashin hukumar NIWA

Majalisar wakilai da kwamitin majalisar dattawa sun gano wasu biliyoyin kudi da aka warewa ma’aikatar National Inland Waterways Agency (NIWA) a shekarar 2017 da 2019.

A cewar kawmitin ayyukan da aka fitar da biliyoyin kudin domin a gabatar da su ba a aiwatar da ko guda daya ba. Majalisar ta gano hakan ne a lokaci da suka yi zama na hadin gwiwa tsakanin kwamitocin majalisar dattawa da na wakilai masu lura da harkokin hukumar.

KU KARANTA:Shugaban majalisa dattawa ya sake gudanar da wani taro kan rashin tsaro a Abuja

An shirya wannan zaman ne domin bin diddigin kasafin kudin shekarar 2019/2020 wanda ma’aikatar sufuri da NIWA suka yi a majalisa ranar Litinin 21 ga watan Oktoba, 2019.

Kamar yadda kwamitin ya fadi, an fitar da naira biliyan 6 domin yin wasu ayyuka da suka shafi sayen kayayyakin aiki na yashe teku da dai sauransu amma babu abu ko daya da akayi.

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Lawan Ahmad ya gabatar da taro game da matsalolin tsaron Abuja a ranar Litinin 21 ga watan Oktoba.

Anyi wani taro makamancin wannan a makon da ya gabata a ofishin shugaban majalisar dattawa domin magance tabarbarewar tsaro a birnin tarayya, Abuja.

Hadimin shugaban majalisar dattawa ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar da yammacin ranar Litinin a Abuja.

https://www.dailytrust.com.ng/just-in-nass-uncovers-dubious-contracts-in-niwas-budgets.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel