Gwamnan PDP ya ziyarci Masallaci domin bawa Musulmai hakuri a kan shirinsa na rushe Masallaci

Gwamnan PDP ya ziyarci Masallaci domin bawa Musulmai hakuri a kan shirinsa na rushe Masallaci

Zababben gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da cewa ya ziyarci wani Masallacin Juma'a na Adogba da ke kan titin Iwo domin tattauna wa da 'yan uwa Musulmi tare da basu hakuri a kan shirin gwamnatinsa na rushe masallacin tare da wani bangare na wata Coci domin gina tashar Mota.

Gwamnan ne da kansa ya sanar da hakan a cikin wasu takaitattun sakonni masu dauke da hotuna da ya wallafa a shafinsa na Tuwita @seyiamakinde.

A cewar daya daga cikin sakonnin gwamnan, "na halarci sallar Juma'a a Masallacin Adogba da ke kan titin Iwo. Na yi magana da 'yan uwanmu Musulmi, Maza da Mata, a kan niyyar gwamnati na rushe Masallacin da wata Coci da sauran wasu gine-gine domin gina katafariyar tashar Mota a kan titin Iwo.

DUBA WANNAN: Mijina ya san ba shine uban yara hudu da na haifa ba saboda ya san ba ya haihuwa - Bazawara

"Na basu tabbacin cewa babu wata manufa ta cin mutunci ko muzanta addini dangane da niyyar gwamnati na rushe Masallaci, tare da yi musu albishir cewa za a canja wa duk wanda abin ya shafa sabon muhalli da kuma biyansa diyya. Na nemi su bawa gwamnati hadin kai domin ta cimma manufofinta."

Da suke mayar da martani a kan sakonnin da gwamnan ya wallafa, jama'a da dama sun yaba masa tare da bayyana cewa yin hakan ita ce hanya mafi dace wa domin kauce wa sabani ko tashin hankali a kan batun rushe Masallacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel