Shugaban majalisa dattawa ya sake gudanar da wani taro kan rashin tsaro a Abuja

Shugaban majalisa dattawa ya sake gudanar da wani taro kan rashin tsaro a Abuja

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, ya sake gudanar da wani taro na musamman kan matsalolin tsaro a babbar birnin tarayya, Abuja.

Anyi wani taro makamancin haka a makon da ya gabata a ofishin shugaban majalisar dattawa don magance lamarin tsaro a birnin tarayya.

Hadimin shugaban majalisar dattawa a kafofin watsa labarai, Ola Awoniyi ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatar a yammacin ranar Litinin.

Yace sabanin ganawar da aka saba yi a baya, ganawar Litinin ya samu halartan Ministan Sadarwa, Isa Ali Ibrahim da kuma Babban darektan hukumar leken asiri na kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar da kuma manyan jami’ai dake da nasaba kai tsaye da harkar tsaron Abuja.

Lawan yace ministan sadarwa ya kasance a taron ne domin nuna cewa mafita ga lamarin zai bukaci shigar da kimiya da fasaha yayin da kasancewar Darektan NIA a taron ya kasance don kula da fannin kasa-da-kasa a matsala tsaron kasa dake fuskantar Abuja.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta batar da kotu domin ta ba da umurnin kwace kadarorina

A cewar jawabin, Lawan ya damu da cewar ya kamata Abuja ta samu ingantaccen tsaro fiye da yadda yake a yanzu, kasancewarta cibiyar mulki.

Wasu sanatocin da suka halarci taron sun hada da Shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi; mataimakin bulaliyar majalisa, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi; Shugaban kwamitin harkokin cikin gida, Sanata Kashim Shettima; Shugaban kwamitin harkokin yan sanda, Sanata Halliru Jika da Sanata Ifeanyi Ubah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel