'Yan daba sun kai tawagar Kwankwaso hari, sun raunata jama'a, sun lalata motoci

'Yan daba sun kai tawagar Kwankwaso hari, sun raunata jama'a, sun lalata motoci

A kalla magoya bayan jam'iyyar PDP tsagin Kwankwasiya 15 aka raunata a ranar Litinin sakamakon harbe-harben bindiga da ake zargin wasu 'yan daba suka yi.

A jawabin da Sanusi Bature Dawakin Tofa, kakakin dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PDP, ya fitar, ya zargi Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kitsa harin da aka kai wa tawagar Sanata Kwankwaso.

Jawabin ya bayyana cewa an kai wa tawagar Kwankwaso harin ne yayin da shi kansa Kwankwaso da tawagar ke dawowa daga kauyen Kwankwaso da ke karkashin karamar hukumar Madobi, inda ya halarci bikin bude wata makarantar horon ma'aikatan lafiya da ya gina.

Jawabin ya cigaba da cewa, "jami'an gwamnatin jihar Kano sun dauko hayar 'yan daba tare da jibge su a daidai gadar Sharada/Sabon Titin Pansheka tun da misalin karfe 1:30 na rana domin kawai su ci zarafin magoya bayan Kwankwaso."

A cewar jawabin, shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wani tsohon hadimin gwamna ne mai suna Murtala Salisu, wanda aka fi sani da 'Gwarmai' shine ya jagoranci 'yan dabar da suka kai harin.

Wasu daga cikin fuskokin 'yan dabar da jawabin ya ce an tabbatar da sune suka kai harin, sun hada da Nazifi Nanaso, Tabo, Ahmadi Babba, Babale Kuffa K/Wambai, Jamilu Goje, Rambo ‘Yanmota Bakin Kasuwa, Dan-Nura Warure, Janwe, Cimutun Dodo, Shehullahi, Isa Dani Badawa, Salo Karota, K.B Soja, Ahmadun Boma Yakasai, Ayi Dan-Allah Sharada, Aminu Mai Talakawa, Musa Baba Dorayi, Umaru Sani Koki, Balele ‘Yanmota Kasuwar Kurmi, Babba Akufi, Babawo Koki, Muntaka Niga Darma, Ma’aru Goma Hanga, Bashir-Go, Danbaba Kofar Mata da Isa Kwanti.

'Yan daba sun kai tawagar Kwankwaso hari, sun raunata jama'a, sun lalata motoci
'Yan daba sun kai tawagar Kwankwaso hari, sun raunata jama'a, sun lalata motoci
Asali: Twitter

'Yan daba sun kai tawagar Kwankwaso hari, sun raunata jama'a, sun lalata motoci
'Yan daba sun kai tawagar Kwankwaso hari, sun raunata jama'a, sun lalata motoci
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel