Yaki da Boko Haram: Buhari zai sayo sabbin jiragen yaki daga kasar Rasha

Yaki da Boko Haram: Buhari zai sayo sabbin jiragen yaki daga kasar Rasha

Fadar gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa gwamnati za ta sayo sabbin jiragen yaki daga kasar Rasha domin ta karfafa yakin da take yi da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, miyagu yan bindiga da sauran miyagun laifuka.

Kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Jiki magayi: Kotu ta sassauta ma Sowore tsauraran sharadin belin da ta gindaya masa

Legit.ng ta ruwaito Garba Shehu wanda yana daga cikin tawar shugaba Buhari da ta wuce kasar Rasha a ranar Litinin domin halartar kasashen Afirka da kasar Rasha da zai gudana a birnin Sochi ya bayyana cewa shugaba Buhari zai tattauna da shugaban Rasha Viladmir Putin domin sayo ma Najeriya sabbin jirage yaki daga kasar.

“Rasha ta kasance abokiya ga Najeriya dake bamu gudunmuwa ta bangaren Soji wajen yaki da yan ta’addan duk da cewa ba wai mun sanyasu cikin maganan yadda ya kamata bane. Don haka wannan ziyara zata bayar da damar daya kamata ga shuwagabannin kasashe biyu su zauna su tattauna musamman game da batun sayan makamai da jiragen yaki.” Inji shi.

Malam Garba ya kara da cewa nan gaba kadan gwamnati za ta bayyana cikakken bayani game da da cinikayyar makaman, sa’annan ya cigaba da cewa kokarin da Najeriya a baya don sayen jiragen yakin daga Rasha ya samu tasgaro ne sakamakon takunkumi da kasar Amurka ta sanya ma Rashan.

Buhari ya samu rakiyar gwamnan jahar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da kuma Gwamna Kayode Fayemi, sa’annan daga cikin ministoci akwai Goeffrey Onyeama, Adeniyi Adebayo, Olamilekan Adegbite da Timupre Sylva

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel