EFCC ta batar da kotu domin ta ba da umurnin kwace kadarorina

EFCC ta batar da kotu domin ta ba da umurnin kwace kadarorina

Tsohon Shugaban Majalisa dattawa, Abubakar Bukola Saraki, yace an yaudari kotun da ta bada umurnin kwace gidajensa dake Ikoyi na wucin gadi ne.

Wata babbar kotun tarayyar dake zama a Legas ta bada umurnin kwace kaddarorin Saaki guda biyu dake a yankin Ikoyi a jihar Legas na wucin gadi bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta nemi hakan.

Amman yayin da yake magana ta hannun hadiminsa, Yusuph Olaniyonu, Saraki yace da shi da lauyoyinsa basu san da wata kara daga hukumar EFCC game da neman umurnin kwace kaddarorin ba.

Yace wata babbar kotun tarayya a Abuja a baya ta bada umurnin hana EFCC daukan kowani mataki akan kaddarorinsa.

Olaniyonu ya bukaci magoya bayan Saraki dasu kwantar da hankalinsu yayin da ake shawo kan lamarin.

A yanzu haka majalisar dokokin jihar Kwara tana gudanar da bincike kan zargin mallakawa Saraki wani gida mai dakuna hudu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta bayar da umarnin kwace wasu kadarorin tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu fadar shugaban kasa na amfani da motocin da aka siya shekara 20 da suka wuce – Sakataren dindindin

Dukkan kadarorin suna yankin Ikoyi ne a jihar Legas. Lauyan hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzik (EFCC), Nnamaeka Omewa, shine ya nufi kotun da bukatar neman ta sahalewa EFCC ta kwace gidajen guda biyu da ke lamba 17A a kan titin McDonald da ke yankin Ikoyi a jihar Legas.

Ya shaida wa kotun cewa Saraki ya mallaki kadarorin ne ta haramtacciyar hanya kuma da kudin da aka samu daga badakala da almundahana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel