Zaben sanata: Melaye da Adeyemi za su fafata a ranar 16 ga watan Nuwamba - INEC

Zaben sanata: Melaye da Adeyemi za su fafata a ranar 16 ga watan Nuwamba - INEC

Za a gudanar da sabon zaben sanatan Kogi ta yammaa tsakanin Sanata Dino Melaye na jam’iyyar PDP da Sanata Smart Adeyemi na jam’iyyar APC a ranar 16 ga watan Nuwamba, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar.

Hukumar INEC a wani jawabi dauke das a hannun Mista Festus Okoye, Shugaban kwamitin bayanai na hukumar, ya bayyana cewa za a hada zaben sanatan ne tare da na gwamnan Kogi.

Okoye, kwamishinan zabe na kasa, a wwani jaabi da ya gabatar ga manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewa za a kuma gudanar da zaben cike gurbi ga mazabar Sabuwa a jihar Katsina a ranar 30 ga watan Nuwwamba.

“Hukumar ta yanke shawarar ne a ganawar da tayi a ranar Litinin,” cewar jawabin.

Ya bayyana cewa sabon zaben ya biyo bayan soke zaben sanata na Kogi ta Yamma da kotun zabe tayi sannan kotun daukaka karat a tabbatar da hakan.

Kotun daukaka kaa ta jaddada hukuncin kotun zabe wacce ta soke zaben Dino Melaye na PDP, biyo bayan wata kara da Sanata Smart Adeyemi na APC ya shigar.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu fadar shugaban kasa na amfani da motocin da aka siya shekara 20 da suka wuce – Sakataren dindindin

Kotun daukaka karan, a ranar 11 ga watan Oktoba ta umurci INEC da ta gudanar da sabon zabe cikin kwwanaki 90 daga ranar da ta yanke hukunci .

Okoye ya roki yan takarar da jam’iyyun da su gudanar da kamfen daidai da tsari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel