Har yanzu fadar shugaban kasa na amfani da motocin da aka siya shekara 20 da suka wuce – Sakataren dindindin

Har yanzu fadar shugaban kasa na amfani da motocin da aka siya shekara 20 da suka wuce – Sakataren dindindin

An siya motocin da ake amfani dasu don gudanar da ayyukan fadar shugaban kasa tun a shekarar 1999, sakataren dindindin na fadar shigaban kasa, Jalal Arabi, ya bayyana.

A bisa wani jawabi da aka saki a Abuja a ranar Litinin daga mataimakin daraktan labarai na fadar shugaban kasa, Attah Esa, yace Arabi ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci tawagarsa zuwa majalisar dokokin tarayyah domin fafatawa kan kasafin kudin 2020.

Sakataren ya kuma kare batun kasafin kudin da ake bukata na fadar shugaban kasar a gaban kwamitin majalisar dattawa kan tarayya da harkokin gwamnati.

Arabi wanda ya gurfana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan ayyuka na musamman yace akwai bukatar gaggawan sauya wadannan ababen hawa domin kula dasu na da matukar wahala.

A cewarsa, kimanin naira biliyan 6.569 aka warewa hakab. Wanda yayi daidai da rage kaso 5.5 da aka ware a kasafin kudin 2019.

KU KARANTA KUMA: Ortom ya bukaci gwamnatin tarayya da ta isar da rufe iyakarta har zuwa kan makiyaya yan kasar waje

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan ayyuka na musamman, Samaila Suleiman, yyinda yake nuna aminta da muhawarar, ya bayar da tabbacin cewa kwamitin zata yi nazari akan muhawaran a tsanaki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel