Ortom ya bukaci gwamnatin tarayya da ta isar da rufe iyakarta har zuwa kan makiyaya yan kasar waje

Ortom ya bukaci gwamnatin tarayya da ta isar da rufe iyakarta har zuwa kan makiyaya yan kasar waje

Gwamnan jihar Benue, Mista Samuel Otom, ya roki gwamnatin tarayya da ta isar da rufe iyakarta har zuwa hana makiyaya daga kasar waje, wadanda ake zargin suna samun damar shigowa garuruwan Najeriya da makamai domin su farma al’umma ciki harda wadanda ke a Benue.

Gwamnan ya yi wannan rook ne a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, lokacin da ya ziyarci wata mata da harin makiyaya ya cika da ita wacce aka yankewa hannu a karshen mako, yayinda take aiki akan gonarta a karamar hukumar Guma, dake jihar Benue.

Ya yi korafin cewa yan Najeriya ba za su iya cigaba da zaman dar-dar a kasarsu ba.

Ortom ya kuma jaddada bukatar haramta duk wani launi na kiwo a bayyane a kasar da kuma samar da filayen kiwo domin kula da kuma tsaro ga dukkanin masu kiwon dabbobi.

KU KARANTA KUMA: Ba lafiya: Yan bindiga sun kai mamaya kauyuka 16, sun kashe yan sa-kai 3 a Kaduna

A wani labari na daban Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce babu wani dalilin takura ko matsi ga wata kasa da ya sanya ta rufe kan iyaka. Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ne ya fadi wannan maganar.

Mr Geoffrey Onyeama ya fadi wannan maganar ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba a Abuja a lokacin da yake ganawa da ministocin kasar Ghana guda biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel