Kotu ta bayar da izinin kwace gdan Bukola Saraki

Kotu ta bayar da izinin kwace gdan Bukola Saraki

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta bayar da umarnin kwace wasu kadarorin tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki.

Dukkan kadarorin suna yankin Ikoyi ne a jihar Legas.

Lauyan hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzik (EFCC), Nnamaeka Omewa, shine ya nufi kotun da bukatar neman ta sahalewa EFCC ta kwace gidajen guda biyu da ke lamba 17A a kan titin McDonald da ke yankin Ikoyi a jihar Legas.

Ya shaida wa kotun cewa Saraki ya mallaki kadarorin ne ta haramtacciyar hanya kuma da kudin da aka samu daga badakala da almundahana.

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya bawa sabbin hadimansa mamaki, ya debi su zuwa hedikwar Boko Haram

A cikin takardar da lauyan ya gabatar a gaban kotun, EFCC ta nemi kotu ta bata izinin kwace kadarorin Saraki na wucin gadi tare da mika su ga gwamnatin tarayya.

Jim kadan bayan saukar Saraki hukumar EFCC ta kai samame gidajen tare da yi musu rubutu da jan fenti, lamarin da ke nuna cewa tana bincike a kansu.

Sai dai, a wancan lokacin, Saraki ya musanta cewa gidajen guda biyu da EFCC ke magana a kansu mallakinsa ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel