Ba lafiya: Yan bindiga sun kai mamaya kauyuka 16, sun kashe yan sa-kai 3 a Kaduna

Ba lafiya: Yan bindiga sun kai mamaya kauyuka 16, sun kashe yan sa-kai 3 a Kaduna

Wasu yan bindiga sun kai hari kauyuka 16 a karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun kashe yan banga uku, wadanda suka shiga daji domin fuskantarsu, yayinda wasu da dama basu dawo ba har yanzu.

Mazauna kauyen da suka yi gudun hijira, wadanda mafi akasarinsu mata, yara da tsoffin ne, na samun mafaka a makarantar Firamare na Birnin Yero a hanyar titin Kaduna-Zaria.

Majiyar tamu ta ruwaito cewa hukumomin tsaro da suka hada da sojoji, yan sanda da jami’an hukumar NSCDC na nan girke a wajen domin hana karya doka da oda.

Hakimin kauyen Anguwar Gide, Malam Jibril Abdullahi, yace yan bindigan sun kai farmaki kauyukansu a maraicen ranar Lahadi sannan suka umurce su da su bar yankin.

“Sun mayar da kauyuka 16 marasa galihu a yanzu haka kuma kauyukan sune Dura, Anguwar Gide, Anguwar Dan Gauta, Anguwar Nayawo, Anguwar Makeri, Jigani, Sabon Gida, Dallatu, Anguwar Ahmadu, Sabon Gari," inji shi.

Hakimin kauyen ya cigaba da bayanin cewa yan bindigan sun kwashe tsawon watanni yanzu suna addabansu, inda hakan ya tursasa mutane kauracewa gonakinsu don gudun kada ayi garkuwa dasu.

‎Wani mazaunin yankin, Salisu Lawal, ya tabbatar da cewar yan bindigan sun kashe yan banga uku.

KU KARANTA KUMA: Gidan Mari: Fursunonin sun kwashe tsawon shekara 8 a daure da sarkoki – Kwamishinar Kaduna

Ya bayyana sunayensu a matsayin Danbirni, Yushehu da Tukur, wanda ya kasance dan hakimin Bakin Kasuwa.

Ba a samu jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ba a waya domin jin ta bakin shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel