Kulle aka yi mani, aka rufe mani kaya, aka yanke mani wuta a gida kamar mai laifi – Achuba

Kulle aka yi mani, aka rufe mani kaya, aka yanke mani wuta a gida kamar mai laifi – Achuba

- Elder Simon Achuba ya bayyana cewa ba aiki da doka a jihar Kogi a halin yanzu

- Tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana yadda ta shi ta kasance a jihar Kogi

Elder Simon Achuba wanda aka tsige daga kujerar mataimakin gwamnan jihar Kogi ya fito ya bada labarin irin halin ka-ka-ni-ka-yin da ya shiga a lokacin da ake ta kutun-kutun din tsige sa.

Mista Simon Achuba ya yi jawabi ne jim kadan daga barinsa kan mulki a Ranar Lahadi 20 ga Watan Oktoba, 2019. Tsohon mataimakin gwamnan ya yi hira da Manema labarai jiya a Lokoja.

Achuba ya koka game da halin da jihar Kogi ta shiga ciki inda yace a yanzu doka da oda sun daina aiki tun bayan da aka tasa shi gaba kamar wanda ya aikata laifi bayan majalisa ta tsige shi.

KU KARANTA: An fadi abubuwan da ya sa aka sauke Mataimakin Gwamna Bello

Tsohon mataimakin gwamnan yake cewa an janye masa jami’an tsaron da ke gadinsa inda aka bar shi wayam a hannun Allah a matsayinsa na Mai daraja ta biyu lokacin a kaf fadin jihar Kogi.

Mista Achuba ya kuma bayyana an datse wutan gidansa sa’ilin da aka sauke shi daga kujera, a lokacin da wani Mai gyara ya yi kokarin gyara wutan, sai sababbin jami’an tsaro su ka hana shi.

Mataimakin gwamnan da ya bar ofis a karshen makon nan yake fadawa ‘yan jarida: “Yanzu haka da na ke yi maku magana, kaya na su na cikin gidan gwamnati. Ba zan iya shiga in dauka ba.”

Sai dai duk da wannan tsohon mataimakin na Yahaya Bello ya nuna cewa ya na sa ran zai yi nasara a kotu inda yake kalubalantar yadda aka tsige shi daga kan kujera ba tare da bin ka’ida ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel