Ganduje: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunce a kan sabbin masarautun Kano

Ganduje: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunce a kan sabbin masarautun Kano

A ranar Litinin wata babbar kotun jihar Kano ta saka ranar 14 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci a kan karar kalubalantar sabbin masarautu hudu da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kirkira.

Wani mutum ne mai suna Rabiu Gwarzo ya shigar da karar shugaban majalisar dokokin jihar Kano, gwamnatin jihar Kano, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kwamishinan shari'a na Kano da shugaban hukumar dab'i ta jihar Kano.

Mai karar na kalubalantar dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta kirkira, wacce ta bawa gwamna Ganduje damar nada karin sabbin sarakunan yanka hudu a jihar Kano.

A yayin zaman kotun na ranar Litinin, lauyan mai kara, Barista AB Mahmud, ya nemi kotu ta bashi damar yin kwaskwarima a kan korafin da ya shigar tun farko.

Sai dai, a nasa bangaren, lauyan shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Louis Mathew-Alozie (mai lambar SAN), ya nuna rashin amincewarsa da bukatar masu kara tare da rokon kotun ta yi watsi da karar saboda rashin ma'ana da wani muhimmanci.

DUBA WANNAN: Kotu ta bawa EFCC izinin kwace kadarorin Bukola Saraki

Barista Yusuf Ali (mai lambar SAN) shine wanda ya wakilci gwamna Ganduje yayin zaman kotun.

Bayan mahawarar lauyoyin ne sai alkalin kotun, Usman Na'abba, ya daga sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci.

An fara sauraron karar ne a wata kotu da ke karkashin jagorancin mai shari'a, Jastis Nasiru Saminu, kafin daga bisani a mayar da ita zuwa kotun Jastis Usman Na'abba wacce ke zamanta a kan titin Miller a unguwar Bompai, karamar hukumar Nasarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel