Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Uba Sani a Kaduna

Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Uba Sani a Kaduna

Kotun daukaka kara, reshen Kaduna a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, ta tabbatar da zabe Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani.

Da yake zartar da hukunci akan karar da Honourable Lawal Adamu na PDP wanda yayi akarar kujerar tare da Uba Sani na APC ya shigar, Justisa A.O. Okojie ya yi watsi da karar aakan hujjar rashin inganci sannan ya kaddamar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lase zaben kujerar sanatan.

Da yake jawabi ga manema labarrai akan hukuncin kotun, daya daga cikin lauyoyin Uba Sani, Barista Frank Ikpe (SAN) ya bayyana hukunci a matsayin mai cike da adalci sannan kuma cewa ya yi daidai da tsarin doka.

A cewarsa hukuncin kotun daukaka karar ya tabbatar da hukuncin kotun zaben sannan y yi bayanin cewa alkalan sun tabbatar da hukuncin akan lamura uku wanda suka hada da ko Uba Sani ya cancanci yin takara, imma na mukamin gwamnati ko kuma rike mukamin siyasa.

KU KARANTA KUMA: Matasan Neja sun yi ga-zanga akan tabarbarewar hanyoyi, sun rufe babban hanyar Minna-Suleja

Ya kara da cewa kotun zaben ta kaddamar da cwa takarardun da mai karar, dan takarar PDP, Lawal Adamu, wanda aka fi sani da Mista LA ya gabatar bai yi daidai da tsarin doka saida ba.

Haka zalika da yake martani kan hukuncin, wani lauyan Sanata Uba Sai, Barista Suleiman Shu'aibu ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga damokradiyya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel