Gobara ta kama a matatar man fetur mafi girma a kasar Iran

Gobara ta kama a matatar man fetur mafi girma a kasar Iran

Gobara ta kama wata matatan mai dake garin Abadan dake jihar Huzistan mai iyaka da lrak a kasar lran. Jihar Huzistan na iyaka da kasar Iraqi.

Kafafen yada labaran gwamnatin kasar Iran sun bada rahoton cewa matatar man fetur mafi girma a kasar ta kama da wuta sakamakon zubewar mai da aka samu.

Jami'an hulda da jama'a na matatar man, Seyin Murbahshi, ya bayyana cewa tuni an kashe wutar kuma babu wani asarar rai ko dukiya mai tsanani.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa da alamun wannan hari ne aka kaiwa kasar saboda yawan hare-haren da ake samu kwanakin baya-bayan nan.

A ranar 14 ga watan Satumbar wannan shekarar ce aka kaiwa Saudiyya hari a kanfanin man kasar mai suna Aramco da jirgi mara matuki da ya haifar da gobarar.

Kasar Amurka da Saudiyya sun daura alhakin wannan gobara kan kasar Iran.

KU KARANTA: Bayan sa'o'i 40, Zakin gidan Zoo na Kano ya koma keji da kansa

Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, Muhammad bin Salman, a hirar da ya gabatar ranar Lahadi ya bayyana cewa fito na fito da kasar Iran zai illanta tattalin arzikin duniya.

Ya bayyana cewa ya gwammace a yi zaman sulhu da siyasa maimakon yaki.

Yarima Mohammed bin Salman ya kara da cewa idan aka shiga yaki a yanzu, farashin danyen mai zai iya tashin da ba'a taba tunani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel