Matasan Neja sun yi ga-zanga akan tabarbarewar hanyoyi, sun rufe babban hanyar Minna-Suleja

Matasan Neja sun yi ga-zanga akan tabarbarewar hanyoyi, sun rufe babban hanyar Minna-Suleja

Wasu matasa a jahar Neja sun yi zanga-zanga akan yanayin tabarbarewar hanyoyi a jahar, sun yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta kawo masu agaji.

Matasan, a bisa wani rahoto daga jaridar Daily Sun, sun toshe babban hanyar Suleja-Minna domin yin zanga-zanga akan lalacewar hanyar wanda motoci ke yawan zirga-zirga akai, inda suka hana ababen hawa shige da fice a Minna.

Jaridar ta ruwaito cewa matasa wanda suka kai kimanin guda 500 sun kasance dauke da kwalayyen sanarwa da rubutu daban-daban.

Jagoran zanga-zangar, Mohammad Etsu, yace ba za a daina zanga-zangar ba har sai ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya zo ya yi masu jawabi.

Wasu daga cikin matasan wadanda suka kasance mambobin kungiyar matasan Najeriya, reshen jahar Neja, ma sun toshe manyan hanyoyin Bida-Minna da Minna-Tegina.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NCC ta amince da yunkurin Airtel na datse cibiyar sadarwar Globacom saboda bashi

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa aukuwar wata gobara a daren ranar Asabar da ta gabata ta salwantar da akalla fiye da shaguna 300 da kuma dukiya ta miliyoyin nairori a kasuwar Santana da ke kan hanyar Sapele a birnin Benin na jihar Edo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, makwabta da mamallakan shagunan ba su samu damar tseratar da dukiyar su a sanadiyar munin da gobarar ta yi/

Wani mazauni da ke makotaka da kasuwar, Monday Ogbeide, ya shaida wa manema labarai cewa, wutar gobarar ta fara ci gadan-gadan ne tun da misalin karfe 11.00 na daren Asabar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel