Shehu Sani ya yi martani akan sace babban jami’in dan sanda

Shehu Sani ya yi martani akan sace babban jami’in dan sanda

- Shehu Sani ya yi matani akan sace wani babban jami’in dan sanda da masu garkuwa da mutane suka yi a Kaduna

- Tsohon dan majalisa yace jami’an yan sandan Najeriya ma na bukatar kariya

Wani Tsohon dan majalisa a majalisar dokokin tarayya ta takwas ya yi martani akan garkuwa da wani mataimakin kwamishinan yan sanda, Musa Rabo da aka yi a anar Asabar, 19 ga watan Oktoba.

Shehu Sani, wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas yace sace Rabo da aka yi ya nuna cewa “jami’an yan sandanmu ma suna bukatar kariya.

Sani yayi sharhin ne a shafinsa na Twitter a aar Litinin, 21 ga watan Oktoba.

Yace: “Jami’anmu ma na bukatar kariya daga masu garkuwa da mutane."

KU KARANTA KUMA: Hukumar NCC ta amince da yunkurin Airtel na datse cibiyar sadarwar Globacom saboda bashi

A halin da ake ciki Legit.ng ta ahoto a baya cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta kasa ta sanar da cewa an kubutar da Musa Rabo, mataimakin kwamishinan 'yan sanda da masu garkuwa da mutane suka sake sace ranar Asabar.

A cewar rundunar, an kubutar da Musa Rabo ba tare da ko kwarzane ya same shi ba, tare da bayyana cewa an kama wasu mutane biyu maza da ake zargi na da hannu wajen sace shi, kuma ana cigaba da bicike.

A cikin wasu jerin takaitattun sakonni da rundunar 'yan sandan ta fitar a shafinta na Tuwita, ta ce wadanda suka sace babban jami'in sun yi amfani da yanayin da yake ciki na farin kaya domin yin garkuwa da shi, tare da bayyana cewa masu laifin basu san waye shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel