Hadimar shugaban kasa ta yi magana yayinda manoma suka yi alkawarin karya farashin shinkafa nan da makonni 3

Hadimar shugaban kasa ta yi magana yayinda manoma suka yi alkawarin karya farashin shinkafa nan da makonni 3

Lauretta Onochie, hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan sadarwa, a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, ta ba yan Najeriya tabbaci akan zargin karya farashin shinkafa a kasuwa.

Onochie wacce ta bayyana hakan a shafinta na Twitter, @Laurestar, tace nan da makonni uku, masu siyan shinkafa “su sanya ran karyewar farashinta zuwa kimanin N9,000 kan kowani buhun 50kg.

Hadimar Shugaban kasar ta yi sharhi ga wani rahoto da jaridar The Punch ta ruwaito inda manoma shinkafa suka yi alkawarin karya farashin shinkafar yayinda suka yi girbi mai tarin yawa.

“Maimakon biyan N25,000 waje siyan shinkafa “yar waje”, za ku samu rarar N16,0000 a shinkafa yar gida domin yin wasu bukatun,” inji Onochie.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NCC ta amince da yunkurin Airtel na datse cibiyar sadarwar Globacom saboda bashi

A yan kwanakin nan, yan Najeriya na ta korafi game da tashin farashin shinkafa, lamarin da wasu ke alakantawa da rufe iyakokin kasar da gwamnatin tarayya tayi wanda aka ce ya hana a shigo da shinkafa yar waje.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci manoman shinkafa a fadin kasar da kada su kara farashin shinkafa sakamakon rufe iyakar kasar da aka yi.

A wani jawabi da ya gabatar a Abuja a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bukaci mambobin kungiyar manoman shinkafa na Najeriya (RIMAN) da sauran masu ruwa da tsaki a sana’ar da kada su boye shinkafa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel