Oluchukwu ya soki Dave Umahi saboda shirin kafa RUGA a Jihar Ebonyi

Oluchukwu ya soki Dave Umahi saboda shirin kafa RUGA a Jihar Ebonyi

- Matakin da gwamna Dave Umahi ya dauka game da tsarin RUGA ya jawo surutu a Ebonyi

- Wani ‘Dan gwagwarmaya a jihar Enugu ya zargi gwamnan da amfani da siyasa a lamarin

Wani fitaccen ‘dan fafutuka ‘dan ainihin jihar Ebonyi, Pascal Oluchukwu, ya dura a kan gwamna Dave Umahi saboda yunkurin da yake yi na gina RUGA a fadin jihar Kudun domin Makiyaya.

Wannan sabon mataki da mai girma gwamna Dave Umahi yake neman dauka bai yi wa Pascal Oluchukwu wanda shi ne shugaban mutanen jihar Ebonyi da ke zama a kasashen ketare dadi ba.

Mista Oluchukwu ya zargi gwamnan da kama layin saida jihar Ebonyi domin abin da zai samu bayan ya bar ofi s a 2023. Oluchukwu ya jefa wannan zargi a kan gwamnan ne a Ranar Lahadi.

Kamar yadda mu ka ji, ‘Dan gwargwamayar ya fitar da jawabi Ranar 20 ga Watan Oktoba yana cewa: Idan gwamna bai janye shirinsa ba, ya shirya fuskantar mummunan martani daga mutane.”

KU KARANTA: Gwamna Umahi ya nemi IGP ya dakaatar da shirin Operation Adder

Ya cigaba da cewa da cewa: “Abin ya isa haka nan. Mu mutanen jihar Ebonyi masu son zaman lafiya ba za mu kyale gwamna Umahi ya saida rayuwarmu saboda makauniyar soyayyar sa ba.”

Wanan Bawan Allah ya na zargin cewa gwamnan na Ebonyi ya na yi wa gwamnatin tarayya makauniyar so ne saboda burinsa na siyasa bayan ya kammala wa’adin gwamna a zaben 2023.

"Mu, mutanen Ebonyi ba za mu kyale wannan kama-karya daga wanda aka ba kaiyyadadden wa’adin mulki ba. Oluchukwu ya yi kira ga gwamnan ya yi maza ya janye mataki da ya dauka.”

“Ba za mu cigaba da yarda da zaluncin da Umahi yake yi wa mutane ba. Yanzu haka an jefa jihar cikin wani hali kuma mun gaji da mugun mulkinsa inda aka shafe watanni babu albashi.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel