Majalisar dattawa ta ki amincewa da kasafin kudin ma'aikatar Neja Delta

Majalisar dattawa ta ki amincewa da kasafin kudin ma'aikatar Neja Delta

A ranar Litinin 21 ga watan Oktoban 2019, kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin yankin Neja Delta, ya yi watsi da daftarin kasafin kudi wanda ma'aikatar Neja Delta da kudirci batar wa a badi.

Majalisar ta ki amincewa da daftarin kasafin kudin ne a sanadiyar wasu manyan ayyuka da ma'aikatar ta cire daga cikin daftarin kasafin kudinta na shekara mai zuwa.

Shugaban kwamitin, Sanata Peter Nwaobishi, ya nemi mambobin kwamitinsa da su bayyana a gaban majalisar a ranar Litinin ta mako mai zuwa domin kare kasafin kudin da ma'aikatar ta kudirci batar wa a shekarar 2020.

Umarnin Sanata Nwaoboshi ya zo ne yayin zaman kare kasafin kudin Najeriya na 2020 wanda ma'aikatu daban-daban ke gudanar wa a babban birnin kasar nan na tarayya.

Sanatan mai wakilcin shiyyar Delta ta Arewa, ya jaddada cewa muhimman ayyukan da ma'aikatar ta cire daga cikin kasafin kudinta na badi, zai kawo tsaikon ci gaba da ayyukan raya yankin Neja Delta da ya kunshi jihohi 9.

Ana iya tuna cewa, a ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2019, majalisar dattawan Najeriya, ta dakatar da zamanta har na tsawon makonni biyu domin bai wa ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin kasar nan damar kare kasafin kudin da suke sa ran batar wa a badi.

Makonni biyu da suka gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudin Najeriya wanda ya wuce naira tiriliyan 10, a zauren majalisar dokokin tarayyar kasar.

KARANTA KUMA: Ko kadan tsoron hukuma ba shi ne dalilin da ya sanya na rufe gidan mari ba - Sheikh Muhammadu Aminu

Haka kuma shugaban kasa Buhari ya ba da umarnin gudanar da binciken kwakwaf kan duk wani shige da ficen kudi kan ayyukan hukumar NDDC mai kula da raya yankin Neja Delta, lamarin da ya ce babu wani abin zo a gani da hukumar ta yi a yankin mai arzikin man fetur.

Shugaban kasa ya bada umarnin fara gudanar da bincike a kan hukumar NDDC tun daga shekarar 2001 har zuwa bana yayin da ya karbi bakuncin gwamnonin jihohin da ke karkashin ikon wannan hukuma a ranar Alhamis ta makon jiya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel