Dakaru sun kashe mutane biyu sanadiyar tsokanar budurwar babban soja a jihar Sakkwato

Dakaru sun kashe mutane biyu sanadiyar tsokanar budurwar babban soja a jihar Sakkwato

Wani rahoto mai ban al'ajabi gami da takaici da muka yakito daga jaridar Daily Nigerian ya bayyana cewa, wani bala'i ya auku a daren ranar Lahadin da ta gabata cikin yankin Mabera dake birnin Shehu wato jihar Sakkwato yayin da wasu dakarun sojin sama suka watsa al'ummar yankin tare da kashe mutane biyu.

Mashaida sun bayyana cewa, wannan takaddama ta auku tun yayin da tsokanar wasu matasan yankin ta fuskata budurwar wani babban jami'i na soja.

Tsokanar matasan yankin ta sanya takaicin duniya ya ishi wannan budurwa wadda hakan ya sanya ta labartawa saurayinta wanda ya kasance babban jami'in tsaro irin abun da ke ci mata tuwo a kwarya.

Gogan naka bai yi wata-wata ba ya aike da mota guda cike da dakaru domin daukar mataki a kan halin kunci da matasan yankin suka jefa masoyiyarsa.

Jaridar Daily Nigerian wadda ta ruwaito rahoton ta ce, sojoji sun bi sahun daya daga cikin matasan wanda ya kasance dalibi, Abdulsalam Lawan, bayan ya tsere har cikin wani gida da ya tare masa hanya.

Sojoji sun banka cikin wannan gida inda suka harbe matashin da kuma wata uwar 'ya'ya bakwai da suka riska mai shekaru 40 a duniya, Maryam Abdulrahman.

Mashaidan wannan mugun ji da mugun gani sun zayyana cewa, wannan ba shi ne karo na farko ba da sojoji suka saba cin zarafinsu.

"A daren jiya muna zaune dai a gaban wani teburin mai shayi da misalin karfe 8.30 na dare, sojojin suka fara harbe-harbe cikin iska inda kuma suka nemi wannan budurwa da ta nuna wadanda ke muzgunawa rayuwarta".

"A yayin da ta gaza gano wadanda ke tsokanarta, sun umarci dukkanin mazauna majalisar ta mai shayi da su yi tsallen kwado. Wadanda kuma suka arce sojojin suka bi su da harbi".

"Kimanin mutane biyar sun raunata a sanadiyar harbi na harsashin bindiga a yayin da mutum biyu kuma suka riga mu gidan gaskiya," inji wani mai bai wa manema labarai shaida, Sani Mabera.

KARANTA KUMA: Zanga Zanga ta barke kan harajin da gwamnatin Lebanon ta sanya a kan amfani da manhajar WhatsApp

Ya zuwa yanzu an killace gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya a babban asbitin birnin Shehu domin gudanar da bincike.

A yayin da manema labarai suka rinka kwarara kira ta hanyar wayar tarho domin jin ta bakin kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Ibikunle Daramalo, bai amsa kiraye-kirayen da aka rinka yi wa wayarsa ba ballanta sakonnin kar ta kwana da aka aike masa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel