Zanga Zanga ta barke kan harajin da gwamnatin Lebanon ta sanya a kan amfani da manhajar WhatsApp

Zanga Zanga ta barke kan harajin da gwamnatin Lebanon ta sanya a kan amfani da manhajar WhatsApp

A rahoton da jaridar BBC Hausa ta wallafa a ranar Juma'a 18 ga watan Oktoba, ta bayyana yadda al'ummar kasar Lebanon suke ci gaba da nuna rashin goyon bayan kudirin gwamnatin kasar na sanya haraji ga masu yin kiran waya ta manhajar WhatsApp.

Duk da cewa gwamnatin kasar ta janye kudirinta na kakaba haraji kan kiran waya ta hanyar amfanin da manhajar sada zumunta ta zamani da ake kira whatsApp, ya zuwa yanzu al'ummar kasar na ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin nuna bacin ransu.

A baya dai gwamnatin kasar Lebanon ta kudiri aniyyar fara karbar haraji na Dalar Amurka 0.20 a kowace rana kan kiran waya ta hanyar amfani da manhajar WhatsApp da sauran manhajojin sada zumunta na zamani.

Daga bisani dai gwamnatin kasar ta janye kudinta jim kadan bayan da lamarin ya haddasa wata mummunar arangama a tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun jikkata a ranar Alhamis ta makon da ya gabata biyo bayan kone-konen tayoyi a kan tintuna da masu zanga-zangar suka yi, lamarin da ya sanya jami'an tsaro suka yi masu tarnaki da 'Tear Gas', wato hayaki mai sanya hawaye wanda wasu ke kira Barkonon Tsohuwa.

KARANTA KUMA: Wani mutum ya mutu yana sassarfa a Legas

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki wanda ake zargin gwamnati ce ta haddasa da ya jefa al'umma cikin halin kunci na rayuwa.

Wani masanin tattalin arzikin na daya daga cikin mutanen da suka gudanar da zangar-zangar, inda yayin ganawa da manema labarai a birnin Beirut ya ce ''Ina zaune a gida sai na ga mutane na zanga-zanga ni ma sai na bi su.

''Ina da aure akwai kudaden da ya kamata a bani duk wata wanda nake bin gwamnati amma ba a bani ba, ga shi bana aiki, laifin gwamnati ne.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel