Gobara ta kona shaguna 300 a kasuwar Benin

Gobara ta kona shaguna 300 a kasuwar Benin

Aukuwar wata gobara a daren ranar Asabar da ta gabata ta salwantar da akalla fiye da shaguna 300 da kuma dukiya ta miliyoyin nairori a kasuwar Santana da ke kan hanyar Sapele a birnin Benin na jihar Edo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, makwabta da mamallakan shagunan ba su samu damar tseratar da dukiyar su a sanadiyar munin da gobarar ta yi/

Wani mazauni da ke makotaka da kasuwar, Monday Ogbeide, ya shaida wa manema labarai cewa, wutar gobarar ta fara ci gadan-gadan ne tun da misalin karfe 11.00 na daren Asabar.

Kawo yanzu an gaza gano ainihin musabbabin gobarar kamar yadda kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito.

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, rundunar 'yan sandan reshen jihar Kano, ta tabbatar da salwantar rayukan wasu mutane uku da suka hadar da miji da matarsa da kuma 'yarsu daya tilo sakamakon gobarar da ta afku a gidansu da ke Unguwar Gayawa Tsohowa a karamar hukumar Ungogo.

KARANTA KUMA: Har yanzu ba a kama Zakin da ya tsere daga gidan adana namun daji a Kano ba

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta jihar, Saidu Mohammed ya ce wadanda suka mutun sun hadar da karamar yarinya wadda ba ta haura shekaru biyu da haihuwa ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel