Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da danta a garin Abuja

Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da danta a garin Abuja

Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata, Misis Hannatu Tukura, tare da danta mai shekara 30 a duniya, Takpeyilo Tukura, a kusa da mararrabar Tiza da ke yankin Kue a babbar birnin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matar wacce ta kasance bazawara, ta kasance matar marigayi Mista Shedrack Tukura, wani sakatarn hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar Nasarawa.

Wani mazaunin yankin, da ya bayyana sunansa a matsayin Benjamin, yace lamarin ya afku ne a ranar Lahadi da misalin 8:12 na dare lokacin da matar, danta, da wata uwa mai shayarwa da kuma wata tsohuwa ke a hanyarsu na tafiya zuwa kauyen Rubochi da ke yankin.

Ya ce Takpeyilo na tuki da suka isa mararrabar, sai yan bindiga suka fito daga daji sannan suka tsare motar da bindiga. Yace yan bindigan sun bude kofar sannan suka umurci matar da danta da su fito daga motar inda suka tafi dasu cikin daji.

Yace har yanzu yan bindigan basu kira ahlinsu ba, k da cewar yace an kai ahoton lamarin gay an sanda a yankin Rubochi.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun tarwatsa sansanin yan bindga guda 2 a jahar Kaduna

Shugaban karamar hukumar Kuje, Abdullahi Suleiman Sabo, ya tabbatar da lamarin.

Kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah, bai amsa kiran da ake masa ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel