Kogi: Dalilan mu na tsige Simon Achuba daga ofis – Inji Majalisar dokoki

Kogi: Dalilan mu na tsige Simon Achuba daga ofis – Inji Majalisar dokoki

Majalisar dokokin jihar Kogi ta fito ta yi karin haske game da tsige mataimakin gwamna Simon Achuba da tayi. Majalisar jihar tace tuni dai bakin alkalami ya riga ya bushe. Jaridar Vanguard.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Kogi, Honarabul Moses Akande ya zargi kwamitin da aka kafa na musamman domin ya binciki tsohon mataimakin gwamnan jihar da yin ba daidai ba a aikinsu.

‘Dan majalisar mai wakiltar shiyyar Ogorimangogo a jam’iyyar APC da yake magana a madadin daukacin majalisar dokokin jihar yace ba a sa wannan kwamiti ta fitar da wata matsaya ba, illa ta yi bincike.

“Kwamitin da aka kafa sun yi aikinsu, sun gabatar mana, mu kuma mu ka dauki mataki. Tsarin aikin shi ne kwamiti za ta yi bincike ne; daukar hukunci ba na ta bane. Kuma haka su ka amince wajen aikin.”

“Daukar matakin cewa mataimakin gwamna ya na da gaskiya ko bai da gaskiya aikin majalisar dokoki ne. Ita kadai ta ke da hurumin bayyana wani aiki ne ya zama ba daidai ba.” Inji Honarabul Akande.

KU KARANTA: PDP ta jefi Jam'iyyar APC da zargi mai karfi ana shirin zaben Gwamna

Majalisar tace sashe na 188(11) na kundin tsarin mulki ya ba ta wannan dama. Akande yake cewa bai san daga inda rahoton kwamitin yake yawo ba bayan da farko shugaban kwamitin ya kira aikin da sirri.

“Akwai alamar tambaya a game da jawabin da ake cewa shugaban kwamitin, Barista John Baiyeshea, ya yi. Idan kwamitin sun mikawa wani daban rahotonsu, ya nuna cewa sun yi wasa da aikin na su.”

Kowa ya san yadda mataimakin gwamnan da aka tsige ya tafi gaban talabijin ya na maganar wasu bayanan sirri, wanda ya sabawa rantsuwar da ya yi, wannan ba babban laifi bane.” Akande ya tambaya.

Majalisar tace Achuba ya yi karya da yace ba a biyansa albashinsa domin hujjoji sun nuna ana biyansa. Aikin kwamiti mu ka yi amfani da shi wajen daukar mataki. Idan bai amince da haka ba, ya tafi kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel