Ku rage farashin sayen Data – Minista Pantami ga kamfanonin sadarwa

Ku rage farashin sayen Data – Minista Pantami ga kamfanonin sadarwa

Ministan sadarwa na Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya umarci dukkanin kamfanonin sadarwa dake Najeriya dasu rage farashin sayen Data da ake amfani dashi wajen shiga shafukan yanar gizo, in ji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Pantami ya umarci hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC ta dabbaka wannan umarni nasa a kan kamfanonin sadarwa ne, sa’annan ya umarci NCC ta dakatar da yadda kamfanonin suke zaftare ma abokan huldansu Data.

KU KARANTA:

Hadimin ministan a kan kafafen sadarwa na zamani, Yusuf Abubakar ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace ministan ya bada wannan umarni ne bayan NCC ta mika masa rahoton ayyukan da suka a gaba da kuma muradunsu na karamin zango.

Ministan ya bayyana damuwarsa game da yadda yan Najeriya ke biyan makudan kudade wajen sayan Data amma basa morewa kamar yadda ya kamata.

“Najeriya bata cikin kasashen Afirka 10 masu saukin Data duk da cewa akwai sama da mutum miliyan 174 dake sayen Data. Haka zalika ga shi sai kamfanonin su dinga zaftare musu Data ba tare da ka’ida ba, ga matsalar network da dai sauran matsaloli.” Inji shi.

A hannu guda kuma, NCC ta nemi ministan ya taimaka wajen kawo karshen wasu daga cikin kalubalen da kamfanonin sadarwar suke fama dashi a masana’antar sadarwa, daga cikinsu akwai sace sacen kayan sadarwa, karancin wutar lantarki, haraji da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel