Ana wata ga wata: Kungiyar ASUU za ta fada yajin aikin sai ‘Baba ta ji’

Ana wata ga wata: Kungiyar ASUU za ta fada yajin aikin sai ‘Baba ta ji’

Kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya, ASUU, ta fara shirye shiryen fadawa wani gagarumin yajin aiki biyo bayan bukatar gwamnatin tarayya na sanya malaman jami’o’i cikin tsarin biyan kudi na bai waya, watau Integrated Personnel Parrol System, IPPIS.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shuwagabannin ASUU sun kira taron gaggawa inda ta nemi rassanta na jahohi su fara tattara yayan kungiyar domin shirin fadawa yajin aiki, a kan wannan bahallatsa.

KU KARANTA:

Idan za’a tuna shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa duk ma’aikacin da bai shiga tsarin IPPIS ba zai daina samun albashinsa. Sai dai shugaban ASUU reshen jami’ar Ibadan, Deji Omole ya bayyana cewa ba wai suna adawa da tsarin gaskiya da gaskiya da tsantseni bane, amma ba zasu zura idanu a keta tsarin cin gashin kai na jami’o’in Najeriya ba.

Omole yace ASUU ta nemi gwamnati ta bata daman gabatar mata da wani sabon tsari da zai kula da matsalolin da malaman jami’o’I zasu fuskanta a karkashin tsarin IPPIS, amma yace gwamnati ta ki amince, ta fi son amfani da tsarin da bankin duniya ta mika mata.

A cewar Omole, IPPIS bai tanadi biyan kudaden karin girma ba, kudin zuwa karo karatu, da wasu alawus alawus, haka zalika yace IPPIS zai kawar da duk wani malamin jami’a daya haura shekaru 60 a maimakon shekarun ritaya na shekara 70 .

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna tirjiya game da rufe iyakokin Najeriya da makwabtanta saboda yana sane da matsanancin halin da tattalin arzikin kasashen zai shiga, don haka da farko bai amince da matakin ba.

Ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba yayin da take ganawa da manema labaru a babban birnin Washington DC na kasar Amurka inda tace an dauke matakin ne don gyara alakar Najeriya da makwabtanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel