Zan cigaba da tallar biredi bayan na tashi daga Ofis - Sabon hadimin gwamnan Zamfara

Zan cigaba da tallar biredi bayan na tashi daga Ofis - Sabon hadimin gwamnan Zamfara

Abdullahi Saidu Maibiredi saurayi ne da Allah ya tarfawa garinsa nono, saboda gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya zabe shi a matsayin mataimaki na musamman a bangaren kafafen sada zumunta.

Saurayin mai tallar biredi ya yi alkawarin cigaba da saida biredinsa duk da wannan daukaka da ya samu.

A wasikar mai kwanan watan 24 ga watan Satumba, 2019, Matawalle ya zabi Maibiredi a matsayin babban mataimaki na musamman gareshi.

A tattaunawar waya da Maibiredi ya yi da jaridar Daily Nigerian, Maibiredi mai shekaru 24 a duniya, ya ce zai cigaba da tallar biredinsa yana tashi daga aiki.

DUBA WANNAN: An kubutar da mataimakin kwamishinan 'yan sanda da masu garkuwa suka sace a daf da Abuja

"Har yanzu ina alfahari da kasuwancina kuma bana jin kaskanci wajen tallata. Na fara siyarda biredi tun ina firamare,"

"Da abinda nake samu daga kasuwancina nake biyan kudin kungiyar malamai da iyaye (PTA), na biya kudin jarabawar kammala firamare da sakandire. Na siyawa kaina keke ina aji 4 na firamare. Bana damun iyayena da bani-bani,"

"Da siyarda biredi na samun kwalin shaidar karatun NCE. A yanzu haka ina shekarar karshe a jami'ar tarayya da ke Gusau. Da hakan na zama abinda na zama a yau. A yanzu haka da muke magana, biredi ne a gabana." In ji maibiredi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel