Aikin jin kai: Dan majalisa ya gina ma tsohuwa yar shekara 70 gida a Zamfara

Aikin jin kai: Dan majalisa ya gina ma tsohuwa yar shekara 70 gida a Zamfara

Duk wanda ya ji tausayin wani, shi ma Allah zai tausaya masa, wannan shine abin da wani dan majalisa mai tausayi ya kwatanta a jahar Zamfara inda ya dauke ma wata tsohuwar mai shekaru 70 a duniya damuwarta.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NNA, ta ruwaito wannan dan majalisa mai suna Kabiru Maipalace kuma shine wakilin al’ummar mazabar Tsafe da Gusau a majalisar wakilan Najeriya dake Abuja.

KU KARANTA: Zaben gwamna: Kada ka kuskura ka taka kafarka a jahar Kogi – PDP ga El-Rufai

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kabiru ta taimaka ma dattijuwa Rakiya Iya ce ta hanyar gina mata gida mai dakuna biyu kyauta a unguwar Tudun Wada dake cikin garin Gusau, kamar yadda hadimin dan majalisar, Mustafa Hassan-Musa ya tabbatar.

Hadimin ya bayyana cewa wannan na daga cikin ayyukan jin kai da maigidansa yake yi domin taimaka ma gajiyayyu da masu karamin karfi a mazabarsa, inda yace dan majalisan ya lura gidan Rakiya ya lalace ne, shi yasa ya kai mata agaji.

“Ba tare da wata wata ba Maipalace ya bada umarnin a gina mata gida mai dakuna biyu, palo, dakin girke girke da kuma ban daki guda daya, a yanzu haka ginin ya kai kashi 90 na kammalawa.” Inji shi.

Daga karshe hadimin yace akwai yankuna da dama da suke cin moriyar ire iren ayyukan alherin Maipalace, inda yace a yanzu haka suna gudanar da ayyukan gina magudanan ruwa da shaguna domin amfanin kananan yan kasuwa a kasuwar Yardole dake Gusau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel