Abin da ya sa hukumar IMF ta goyi bayan rufe iyakoki - Zainab Ahmed

Abin da ya sa hukumar IMF ta goyi bayan rufe iyakoki - Zainab Ahmed

Duk da koke-koken da ake yi, Ministar kudin Najeriya, Misis Zainab Ahmed, ta bayyana cewa hukumar IMF mai bada lamuni a Duniya ta na goyon bayan rufe iyakokin kasa da Najeriya ta yi.

Zainab Ahmed ta yi wannan jawabi ne lokacin da ta yi wata zantawa da Manema labarai a babban birnin Washington na kasar Amurka a yammacin jiya Ranar Lahadi 20 ga Watan Oktoba, 2019.

Ministar kudi da kasafin kudin Najeriyar ta ke cewa hukumar IMF ta na goyon bayan wannan mataki na gwamnatinsu domin kuwa an fahimci ba an yi hakan bane domin a muzgunawa kowa.

Ahmed ta ke cewa da farko shugaba Muhammadu Buhari bai karbi tayin rufe kan iyakokin ba domin ya san irin halin da kasashen da ke mu’amalar kasuwanci da Najeriya za su shiga ciki.

A cewar Ministar Najeriyar, an rufe kan iyakokin kasar ne domin babbako da alakar da Najeriya ta ke da shi da kasashen da ke makwabataka da ita kamar yadda aka cin ma yarjejeniya tun asali.

KU KARANTA: Za a ba Gwamnatin Tarayya bashin kudi domin gyara wutar lantarki

“Mun zauna da Makwabtanmu waje ganin an bi dokoki, amma abubuwa kara cabewa su ka yi. Babu shakka, wannan zai jefa kasashen da ke kusa da mu cikin wani halin tattalin arziki.”

Ministar ta bayyanawa Duniya cewa: “Hukumar IMF ta na goyon bayan rufe iyakokin da mu ka yi domin sun fahimci cewa ba an rufe iyakokin bane domin keta. Sai don cika alkawarin da aka yi.”

“Yarjejeniyar mu da kasashe ita ce, kayayyaki za su shigo mana ne kurum ta tashoshin inda za a kawo su a daure har nan, sai jami’an da ke maganin fasa-kauri su duba, su karbi kudin shiga.”

“Amma ba abin da ke faruwa ba kenan, ana shigo da kaya a bude, ana kuma bari ana yin fasa-kauri ta barayin hanyoyi.” Ahmed tace su na goyon bayan kasuwanci tsakanin kasashen Nahiyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel