Zaben gwamna: Kada ka kuskura ka taka kafarka a jahar Kogi – PDP ga El-Rufai

Zaben gwamna: Kada ka kuskura ka taka kafarka a jahar Kogi – PDP ga El-Rufai

Jam’iyyar adawa ta PDP reshen jahar Kogi ta gargadi gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa’i da kada ya kuskura ya taka kafarsa a jahar a yayin gudanar da zaben gwamnan jahar, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa dya fitar, inda ya yi kira ga El-Rufai daya shawarci Gwamna Yahaya Bello ya dauki dangana da kayin da zai sha saboda PDP ce za ta lashe zaben 16 ga watan Nuwamba, a cewarsa.

KU KARANTA: Za mu tashi jami’ar jahar Kaduna daga inda take – Gwamnatin Kaduna

PDP ta yi ikirarin cewa Yahaya Bello ba zai iya nuna wani aiki guda daya gudanar ba tun bayan hawansa kujerar gwamna, jam’iyyar ta kara da cewa Gwamna Bello ya mayar da jahar Kogi koma baya ta zama matalauciyar jaha a Najeriya.

“Idan APC da gaske tana son Kogi da alheri, bay akin neman zabe ya kamata ta fara ba, kamata ya yi ta shawarci Yahaya Bello ya yi amfani da sauran kwanakin da suka rage masa wajen saduda bisa abubuwan da ya yi ma jama’an jahar.

“Ya biya ma’aikata da yan fansho albashinsu na watanni 36, tare da neman gafarar mutanen da suka mutu a sanadiyyar mulkin zaluncin da yake yi a jahar, sa’annan kuma ya shirya takardun mika mulki, ya kamata majalisar yakin neman zaben APC ta sani jama’an Kogi sun yanke hukuncin saka ma kura aniyarta a kan Yahaya Bello ta hanyar sallamarsa daga Ofis.” Inji shi.

Idan za'a tuna a makon data gabata ne dai jam'iyyar APC ta nada Gwamna El-Rufai a matsayin jagoran kwamitin yakin neman zabe na gwamnan jahar Kogi, inda El-Rufai ya yi alkawarin tarewa a Kogi tun da wuri don gudanar da shirye shiryen kawo kujerarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel