An kubutar da mataimakin kwamishinan 'yan sanda da masu garkuwa suka sace a daf da Abuja

An kubutar da mataimakin kwamishinan 'yan sanda da masu garkuwa suka sace a daf da Abuja

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kasa ta sanar da cewa an kubutar da Musa Rabo, mataimakin kwamishinan 'yan sanda da masu garkuwa da mutane suka sake sace ranar Asabar.

A cewar rundunar, an kubutar da Musa Rabo ba tare da ko kwarzane ya same shi ba, tare da bayyana cewa an kama wasu mutane biyu maza da ake zargi na da hannu wajen sace shi, kuma ana cigaba da bicike.

A cikin wasu jerin takaitattun sakonni da rundunar 'yan sandan ta fitar a shafinta na Tuwita, ta ce wadanda suka sace babban jami'in sun yi amfani da yanayin da yake ciki na farin kaya domin yin garkuwa da shi, tare da bayyana cewa masu laifin basu san waye shi ba.

Tawagar jami'an 'yan sanda daga jihohin Kaduna, Neja, da Abuja sune suka hadu da na wata rundunar 'yan sanda ta musamman domin kubutar da Rabo da yammacin ranar Lahadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel